Take a fresh look at your lifestyle.

Kaduna Ta ware Kananan Hukumomi 13 Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

115

Sakataren zartarwa na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) Dakta Usman Mazadu ya bayar da tabbacin cewa an dauki isassun matakan dakile illar ambaliyar ruwa a jihar a lokacin damina ta 2025.

Mazadu ya bayyana haka ne a Kaduna a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirin hukumar na duk wani lamari na gaggawa da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a a yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa.

Ya ce matakan sun yi daidai da umarnin Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna na ba da fifiko ga tsaron lafiyar mazauna yankin musamman ma al’ummomin da Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ambaliyar ruwa.

Gwamnatin jihar ta samar da kayayyakin sansani ga Cibiyoyin Safe Haven a fadin kananan hukumomi 13 da NiMet ta bayyana cewa suna da hatsarin gaske.

“Bugu da kari mun yi tanadin isassun kayan abinci a cibiyoyin tare da tanadin kayan agaji don magance duk wani bala’i cikin gaggawa,” in ji shi.

Shugaban SEMA ya ce hukumar ta dauki tsawon makonni shida tana gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa a cikin al’ummomi Da abin ya shafa.

Ya bukaci mazauna yankin da su guji yin gini ko zubar da shara a magudanan ruwa da bakin kogi wanda hakan na iya kara ta’azzara ambaliya ruwa.

“Muna kira ga ‘yan kasa da su goyon bayan gwamnati ta hanyar bin ka’idojin tsaro da kuma taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi” in ji Mazadu.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.